Showing posts with label Dadin Kowa. Show all posts
Showing posts with label Dadin Kowa. Show all posts

Sunday, 5 May 2019

VIDEO: Dadin Kowa Sabon Salo Episode 104 AREWA24

Kura ta kai bango a bangarori da dama a garin Dadin Kowa, Stephanie ta budewa Samuel wuta, yayin da Kamaye shima ya budewa Adama tasa wutar. A bangare guda Zayad ya bude tasa wutar ne ga babban abokin hamayyarsa Rabe, shin waye zai ci nasara? Lokaci ne zai nuna.

Friday, 3 May 2019

VIDEO: Dadin Kowa Sabon Salo Episode 103 AREWA24

A lokacin da Kamaye ke jimamin mutuwar Hannatu, garin Dadin Kowa ya dau zafi inda hukuma ta dau alwashin yashe duk wani bara gurbi a garin, wanda ta kira da OPERATION TSAME NAMA. Su wa za’a tsame a Dadin kowa?

VIDEO: Dadin Kowa Sabon Salo Episode 102 AREWA24

Hannatu na kan gwiwa, nakuda ta zo da gardama, asibiti na bukatar kudi, Kamaye ba kudi babu dalilinsu, abin da ya rage a yanzu shine wata 'yar tunkiyar Adamu da take kiwo ita za'a sayar, kuma ko da an sayar din kudin ba zasu isa ba. Wannan ita ta sanya Kamaye ya bazama neman kudin da zasu bkai Hannatu asibiti ko ta halin Kaka, to sai daikuma a inda yake tsammanin zai samu kudin ba ta nan ya samu ba, haka nan samun kudin bai hana wankin hula ya kai su dare ba.

Monday, 15 April 2019

VIDEO: Dadin Kowa Sabon Salo Episode 101 AREWA24

A lokacin da Rabe ke kokarin ganin ya fadada da'irarsa a wannan lokacin abubuwa sukakara cakude masa, yayin da a bangare guda yunkurin Adama na karshe akan ganin ta halakaabun dake cikin Hannatu ya faskara.

Tuesday, 9 April 2019

VIDEO: Dadin Kowa Sabon Salo Episode 100 AREWA24

Dadin Kowa Sabon Salo Episode 100 AREWA24

Sunday, 31 March 2019

VIDEO: Dadin Kowa Sabon Salo Episode 99 AREWA24

Da sanyin safiya Adama ta kai karar Sabuwa ofishin 'yan sanda, bisa zargin ta lakada mata dan banzan duka, sai dai kuma bayan da Sabuwa ta ziyarci ofsi din ''yan sandan, sai wani sabon rikicin ya sake barkewa, inda Sabuwa ta dunkule hannu ta na kokarin kai Adama wani sabon naushin a gaban hukuma.

Tuesday, 26 March 2019

VIDEO: Dadin Kowa Sabon Salo Episode 98 AREWA24

Al’amura sun ci gaba da dagulewa a garin dadin kowa, a wani bangare Yesmin babbar kawar Bintu na kokarin ta mayar da ita ruwa ta hanyar kawo mata kayan maye har gida, to sai dai kuma I.b wanda ke da burin auren Bintu ya taka wa Yesmin birki, da alkawarin in ya sake ganinta da da Bintu sai ya kakkaryata.
A wani bangare kuma Adama ta yi amai ta lashe, inda ta nemi Danmagori ya tayar da kwantaccen cikin Hannatu a kokarin da take na ganin Hannatu ta auri Ayuba maigadi. Hakan bayan alkawarin da kamaye ya yi ne cewa ba za a taba aurar da Hannatu ba har sai ta haihu.