Yajin Aiki: Kungiyar ASUU Ta Za Koma Teburin Sulhu Da Gwamnati Kungiyar Malaman jami’o’in Nijeriya (ASUU), za ta koma teburin sulhu tare da gwmnatin tarayya a gobe Litinin domin ci gaba da yunkurin kawo karshen yajin aikin da malaman jami’a suke yi fiye da tsawon watanni biyu da suka gabata.
Shugaban kungiyar ASUU na kasa, Farfesa Biodun Ogunyemi, ne ya bayyana hakan a wata ganawa da yayi da manena labarai a Birnin Abuja a ranar Juma’ar da ta gabata.
Rashin cika alkawuran gwamnatin tarayya ya sanya kungiyar ke ci gaba da tayar da kayar baya da nuna fushin ta gami da gajon hakuri kamar yadda Farfesa Ogunyemi ya bayyana.
Kungiyar ASUU ta afka yajin aiki na sai baba-ta-gani tun a ranar 4 ga watan Nuwamba na shekarar da ta gabata sakamakon kiraye-kirayen ta da neman inganta ci gaba da kuma habakar jami’o’in kasar nan musamman ta fuskar gine-gine da kayan karatu na zamani.
Kungiyar ASUU na ci gaba da neman gwamnatin tarayya ta biya musa bukatunsu cikin yarjejeniyar da suka kulla da gwamnatin tarayya a tsakanin shekarar 2012 zuwa 2017.
Gabanin zaman da kungiyar ASUU za ta gudanar tare da gwamnatin tarayya a gobe litinin, sun gudanar da zaman sulhu tsakanin su daban-daban har sau hudu tun bayan yajin aikin da malamai suka afka amma har yanzu hakar su ba ta cimma ba ruwa ba.
A halin yanzu ana ci gaba da zargin juna kan rashin haifar da da mai ido tsakanin kungiyar ASUU da kuma gwamnatin tarayya kan rashin kawo karshen yajin aikin malaman jami’o’in Nijeriya suke yi.

EmoticonEmoticon