Monday, 21 January 2019

INEC Ta Fitar Da Jerin Sunayen ‘Yan Takara Na Karshe

Tags

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa wato INEC ta fitar da sunayen ‘yan takarar da za su kasance a cikin zaben 2019 da zai gudana.

Wannan jerin sunaye shi ne karo na karshe da hukumar ta fitar. Wanda hakan ke nufin in dai ba ka ga sunan dan takara ba, ba ya cikin wadanda za su kasance cikin zaben 2019.

Sunayen da INEC din ta fitar sun hada da sunayen ‘yan takarar shugabancin kasa, Majalisar Dattawa, ‘yan majalisar tarayya da na jiha. Wannan jerin sunayen hukumar ta wallafa shi ne a amintaccen shafinta na Twitter @inecnigeria.

Akwai sunayen ‘yan takarar shugabancin kasa da mataimakansu 144 daga jam’iyyu daban-daban. Sai dai a jam’iyyar SDP ba su ayyana sunan kowa ba, tun kama daga dan takarar shugabancin kasar zuwa mataimaki, sakamakon yadda rigima ta kaure tsakanin ‘yan takarar guda biyu a karkashin jam’iyyar, wanda ya hada da; tsohon ministan labarai, Jerry Gana, da kuma tsohon gwamnan jihar Kuros Ribas, Donald Duke, inda kowa ke jin cewa shi ked a tikitin tsayawa takarar.

Wannan ya faru ne sakamakon yadda kotun ta tabbatarwa da Jerry Gana takarar, a yayin da ita kuma jam’iyya ta zabi Donald Duke a matsayin dan takararta. A cikin jerin sunayen da INEC din ta fitar akwai sunayen mata 28 wanda ya kasance ko dai sune ‘yan takarar ko kuma suna matsayin mataimakiya.

Sannan akwai mai shekaru 30 mai suna Johnson Omede, a matsayin mataimakin shugaban a karkashin jam’iyyar NNPP. Wanda shi ne mai kananan shekaru a cikin dukkanin ‘yan takarar shugabancin kasar da mataimakansu.

Akwai dai ‘yan takarar shugabancin kasa guda 72 a jam’iyyu daban-daban tare da masu taimaka musu su ma guda 72. Sunan ‘yan takarar shugabancin kasar, sun hada shugaban kasa Muhammadu Buhari da mataimakinsa Yemi Osinbajo, a karkashin jam’iyyar APC. Sai ‘yan jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, da mataimakinsa Peter Obi.

Sauran sun hada da Oby Ezekwesili daga jam’iyyar APMN, sai Omoyele Sowore a jam’iyyar AAC sai kuma Kingsley Moghalu a jam’iyyar YPP, sai kuma Sina Fagbenro-Byron a jam’iyyar KOWA Party.

Akwai kuma Fela Durotoye a jam’iyyar ANN. Sauran har wala yau sun hada da; Obadaiah Mailafia a jam’iyyar ADC, sai Misis Eunice Atuejide daga jam’iyyar NIP da dai sauran su.


EmoticonEmoticon