Shugaba kasa Muhammadu Buhari ya cire babban sakataren Asusun tallafawa manyan makarantu na Nijeriya (TETFund), Dr. Abdullahi Baffa Bichi.
Rahotanni sun bayyana cewa an maye gurbinsa da tsohon sakataren hukumar, Farfesa Elias Suleiman Bogoro.
Kafin nadinsa a matsayin sakateren hukumar tare da wasu shugabanin hukumomi 14 a ma’aikatar ilimi a ranar 2 ga Augustan 2016, Baffa ya kasance hadimi ne ga Ministan Ilimi na kasa, Adamu Adamu.
Mun samu labari cewa cikin ‘yan kwanakin nan, ana samun rashin jituwa tsakanin Dr. Baffa da ministan Ilimi, Adamu Adamu musamman dangane da kudaden tallafi na 2019.
Rahotanni sun bayyana cewa basa samun jituwar da ministan a kan batutuwa da yawa da ake gudanarwa a karkashin TETFund musamman batun kudaden tallafin jami’o’i.
Bugu da kari, Baffa ya kasance yana shiga cikin harkokin siyasar jihar Kano dumu-dumu gabanin babban zaben da ke tafe a watan Fabrairu.

EmoticonEmoticon