Shugaban Kwamitin yada Labaran takarar Gwamnan Dakta Abdullahi Umar Ganduje, Malam Muhammad Garba ya bayyana dalilin da ya Sanata Rabiu Musa Kwankwaso kasa sake tsayawa takarar Kujerar Sanatan Kano tsakiya da cewar tsoron kar tsohon Gwamnan Kano Malam Ibrahim Shekarau ya rangada shida kasa ne.
Malam Muhammad Garba ya bayyana haka ga manema labarai ne a lokacin da kwamitin yakin neman zaben Gwamna Ganduje ya ziyarci Karamar Hukumar Karaye ranar Lahadin data gabata, inda ya bayyana kwankwaso da cewa yanzu siyasar Kwankwaso ta zo karshe.
A cewar Malam Muhammad Garba wanda kuma shi ne kwamishinan ma’aikatar yada labarai ta Jihar Kano, Kwankwaso ya gani kurukuru da idonsa a rubuce jikin katangu cewar faduwa ta tabbata gareshi, wanda hakan tasa cikin hikima ya janye takarar tasa domin tsoron fuskanatar gagarumar kunya alokacin da Shekarau zai rangada shi da kasa.
Idan za’a iya tunawa Malam Ibrahin Shekarau a shekara ta 2003 da shekara 2007 ya nunawa kwankwaso iyakarsa lokacin da shekarau ya kayar dashi alokacin yana kan kujerar Gwamna hakan kuma ta kara furuwa a shekara ta 2007 lokacin da aka sake kayar da dan takarar Kwankwaso a zaben shekara ta 2007.
Malam Muhammad Garba ya ci gaba da cewa ficewar da makusantan Kwankwaso ke yi suna komawa cikin Jam’iyyar APC ke tabbatar da faduwar dan takarar Gwamnan da Kwankwaso ya tsayar tun kafin lokacin zaben.
Haka suma sauran da ke nuna suna tare da Kwankwaso kwai suna yin hakan ne domin kawar da hankalin Kwankwaso, domin ganin yadda ya dauko surikinsa ya kakabawa Kwankwasawan da Jam’iyyar PDP wanda ba zabin ‘yan Jam’iyyar PDPin ba ne. Shugaban Kwamitin yada labaran takarar Gwamna Gandujen ya ci gaba da bayyana cewa sabon salon nasarorin da Gwamna Ganduje ke samu ‘yan manuniya ce dake tabbatar da toshewar duk wata kofa da Kwankwaso zai iya tallata dan takarar tasa.
Don haka sai Malam Muhammad Garba ya shawarci Kwankwaso da Jam’iyyar PDP su hadiya batun burinsu su rungumi kaddarar faduwa zabe domin kanawa anyi walkiya sun gansu.
Ya ce tuni muka kimtsa tsaf domin tunkarar mataki na gaba, don haka muke kara damara domin kara himmatuwa wajen ci gaba da samar da cigaban da ake bukata a shekaru hudu nan gaba, shirin mu shi ne sake dawo da kimar Kano da Kanawa ta fuskar rike kambun Jihar na cibiyarar tattalin arziki, saboda haka muna godiya kwarai bisa goyon bayan da mutanen Kano ke baiwa wannan Gwamnati, muna tabbatarwa da Kanawa cewa ba za’a basu kunya ba.

EmoticonEmoticon