A jiya ne Shugaba Buhari ya bayar da dalilansa na kin halartar muhawarar ‘yan takaran Shugabancin kasa wanda hukumar shirya muhawarar ‘yan takaran shugabancin kasa da kafar yada labarai ta kasa (BON), suka shirya.
Mai magana da yawun kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na Jam’iyyar APC, Barista Festus Keyamo, ya ce, Shugaban kasa bai halarci muhawarar ne ba saboda ayyukan da ke gabansa da suka yi taho mu gama da lokacin gudanar da muhawarar, da kuma kasantuwar ya halarci wani taro tare da al’umma wanda hakan ya ba shi daman musayar ra’ayi tare da ‘yan Nijeriya kai tsaye.
“Da farko dai, daga cikin daman da dan takaranmu ya samu na ya gana da ‘yan Nijeriya kai tsaye, dan takaran na mu ya yi amfani da wannan daman wajen halartar wani taro na al’umma wanda wata kungiya ta shirya wanda ya gudana a ranar Laraba, 16 ga watan Janairu, 2019.
“Tare da shi a wajn tattaunawar akwai Mataimakin Shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo. ‘Yan Nijeriya daga ko’ina da suke a wajen da kuma ta yanar gizo sun yi tambayoyi a kan mahimman batutuwa. An kuma yada abin kai tsaye a kafafen yada labarai masu yawa na Nijeriya,” in ji shi.
Festus Keyamo, ya kara da cewa, ayyuka kuma masu yawa na ofis duk suna gaban shugaba Buhari, kuma sun yi dace da lokacin gudanar da muhawarar.
A jiya ne, Shugaba Buhari ya kaddamar da tashar ruwa ta Baro, a Jihar Neja, da kuma yakin neman zaben da ya je a Jihohin Neja da Filato, inda yawan jama’a ya jinkirta lokacin na shi a duk Jihohin biyu, sai can da yamma ne ya iya komowa Abuja.
“Amma muna godiya ga wadanda suka shirya muhawarar a bisa gayyatar da suka yi mana, muna kuma tabbatarwa da ‘yan Nijeriya za mu ci gaba da martaba wadannan kungiyoyin masu shirya muhawara irin wannan wanda dan takaranmu ya yi amfani da ita a lokacin muhawarar zaben da ya shige.
‘‘Yan Nijeriya za su iya tunawa a ‘yan makwannin da suka shige, Mataimakin dan takaran shugabancin kasar Jam’iyyarmu, Farfesa Yemi Osinbajo, ya halarci Muhawarar da ita dai wannan kungiyar ta shirya,” in ji shi.
Ya kara da cewa, maganar da Atiku ya yi alhalin babu Buhari a wajen, ya nuna cewa, shi da Jam’iyyar sa ta PDP, ba su da wani abin da za su iya tabukawa Nijeriya.

EmoticonEmoticon