Kevin-Prince Boateng ya koma Barcelona aro daga Sassoulo zuwa karshen kakar bana, an kuma gabatar da shi a gaban magoya baya a Nou Camp a ranar Talata.
Boateng zai taka-leda aro wata shida a Barcelona kan Yuro miliyan daya da yarjejeniyar biyan kungiyar Italiya Yuro miliyan takwas idan ya taka rawar gani.
Dan wasan mai shekara 31 zai rinka maye gurbin Luis Suarez ko Lionel Messi idan an samu wata matsala, bayan da ta sayar da Munir El Haddadi ga Sevilla a farkon makon nan.
Boateng zai cika shekara 32 a watan Maris ya kuma buga wa kungiyoyi 10 tamaula, ciki har da AC Milan da Borussia Dortmund da Tottenham da kuma Portsmouth.
Haka kuma yana da kwarewar buga gasar La Liga, bayan da ya yi wa La Palmas wasa a kakar 2016/17.
Barcelona wadda Ernesto Valverde ke jagoranta ta yi karawa 31 a kakar bana, ita ce ta daya a teburin La Liga, tana buga gasar Zakarun Turai da ta Copa Del Rey.

EmoticonEmoticon