Hukumar ‘Yan sanda ta bayyana cewa, yanzu haka an mika takardun neman aikin dan sanda guda dubu dari biyu da arba’in da biyu da dari hudu da hansin da biyar, wanda wannan ya nunka adadin da ake bukatar dauka na mutun dubu goma.
Majiyarmu ta shaida mana cewa, Hukumar ta karbi takardun neman shiga aikin na mutum dubu dari da hamsin da takwas da dari bakwai da saba’in da uku kwana goma sha biyu kadai fara karbar takardun.
Majiyar ta mu ta ci gaba da shaida mana cewa, shugaban kasa muhammadu Buhari ya amince a dauki karin ‘yan sanda dubu goma a kwanan nan, yadda za a kara musu karfin tabbatar da zaman lafiya a kasa baki daya.
Mukkaddashin jami’in hulda da jama’a na Hukumar ne Mista Aaron Kaase ya bayyana haka ranar Alhamis din da ta gabata a Abuja, ya ce dukkan wadannan takardu an same su ne cikin mko hudu da fara karbar takaradun bukatar. “Ya kuma ci gaba da cewa za su rufe karbar takardun ne bayan mako shida, kamar yadda doka ta tanada,” in ji shi.
Ya ce jihar Neja ita ta fi kowace jiha inda mutum dubu goma sha biyar da dari shida da talatin da uku suka nemi aikin sai jihar Kano mai dubu goma sha biyar da saba’in da biyar daga nan sai Katsina dubu goma sha hudu da dari biyar da tamanin da biyu Bauchi dubu goma sha biyu da dari shida da hamsin da biyu sai Kaduna dubu goma sha uku da dari takwas da tamanin da biyu sannan Adamawa mai dubu goma sha daya da dari hudu da arba’in da tara.
Jami’in hudda da jama’ar ya ci gaba da cewa, jihar Bayelsa ita ma fi karancin mutanen da suka nemi aikin wato su 1, 258, sai Legas mai mutum 1, 358, sai Ebonyi mai mutum 1, 659 da kuma Anambra mai 1,618.
Kaase ya ce cikin mutum 242, 455 da suka nemi aikin, mutum 212, 716 maza ne sai kuma mata su 29, 694.
Ya ce jihar Benuwe ita ta fi yawan matan da suka nemi aikin in suka kai su 2,251, sai Akwa Ibom mata 1, 772. Jihar Osun it ace ta uku mai 1,721, yayin da jihar Zamfara kuma ta zama ta karshe mai mata 27. Ya ce shugaban Hukumar Mista Musiliu Smith ya sa ido sosai ganin cewa sai wadanda suaka cancanta ne kawai za a dauka aikin.
Source: hausa.leadership.ng

EmoticonEmoticon