Shugaban rikon kwarya na Hukumar yaki da cin-hanci da rashawa da yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa EFCC Mista Ibrahim Magu, ya sanar da cewar hukumar za ta kara kaimi a cikin shekarar 2019 don tabbatar da hukunci da yawa.
Mista Ibrahim Magu ya bayyana hakan ne a cikin sanarwar da Kakakin hukumar na rikon kwarya Mista Tony Orilade ya fitar a ranar Alhamis a garin Abuja.
Mista Ibrahim Magu wanda ya ya yi alkwarin a lokacin da ya kai ziyarar aiki a ofishin hukumar da ke jihar Legas ya ci gaba da cewa, yanke hukunci guda 312 da aka yi a shekarar 2018, mun shirin rubanya hakan a shekarar 2019.
Ya ci gaba da cewa wannan shi ne kokarin da muke son mu cim ma bari don mu kawar da mummunar fahimtar da wasu suke yiwa hukumar a kan yaki da cin hanci da rashawa.
Mista Ibrahim Magu ya bayyana cewar, hukumar ta EFCC ta nemo yanke hukunci uku a cikin wannan sabuwar shekarar inda ya yi nuni da cewar wannan wani babban mataki ne na farko.
A cewar sa, hukumar ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen rage cin-hanci da rashawa a kasar nan da kuma yin safafar kudi ta haramtacciyar hanya.
Ya sanar da cewar, hukumar a shirye take wajen gudanar da ayyukan ta daidai da yadda aikin yake a fadin duniya da kuma yadda doka ta tanada.
Ya yabawa Shugaban Alkalai na kasa Mai Shari’a Walter Onnoghen, a kan nasarar da hukumar ta samu a shekarar da ta wuce inda ya yi nuni da cewar fannin shari’a ya taka rawa sosai wajen yaki da cin hanci da rashawa a kasar nan.
Ya yi nuni da cewa, ya kamata mutane su sami cewar aikin Hukumar shi ne ta cafko masu cin-hanci,inda kuma bangaren shari’a ne ke da hakkin hukunta su, inda ya yi nuni da cewar ba don fannin shari’ar ba, zai yi wuya muci nasarar da muka samu a shekarar 2018 ba, muna kuma son mu rubanya nasarar a shekarar 2019.
Shugaban ya kuma yi kira ga sauran masu ruwa da tsakida sauran yan Nijeriya dasu hada kai da hukumar don rage cin-hanci da rashawa a kasar nan.
Acewar Mista Ibrahim Magu, wadanda suka saci dukiyar yan kasa su sani cewar basu da wani wajen boyo, inda ya ce, domin hukumar ta ba za komar ta wajen cafko dukkan wanda ake zargin ya ci-hanci da rashawa.
Source: hausa.leadership.ng

EmoticonEmoticon