Wednesday, 9 January 2019

Jama’a Ba Za Su Yi Nadamar Sake Zaben Jam’iyyar APC Ba - Gwamna Masari

Tags

Gwamnan Jihar Katsina Alhaji Aminu Bello Masari ya bada tabbacin cewa idan ‘yan Najeriya suka sake zaben jam’iyyar APC a wannan zaben mai zuwa ba za su yi nadamar yin hakan ba.

Gwamna Masari yana magana a gaban dandazun magoya bayan jam’iyyar APC a wajan gangamin yakin neman zabensa karo na biyu da ya gudana a kananan hukumomin Matazu da Musawa domin tunkarar zabe mai zuwa.

Kamar yadda ya bayyana a karkashin jagorancin gwamnatin APC an kawo canji mai ma’ana wanda ya canza rayuwar ‘yan Najeriya ta yau da kullin inda ya kara da cewa mafiyawancin alkawarin da suka dauka a shekarar 2015 sun cika saura kuma suna kan hanya cikawa Sannan ya bada tabbacin cika alkawari da jama’ar suka roka a wannan yakin neman zabe na shi, da zaran an samu nasasar lashe zabe a wannan zabe mai zuwa.

Haka kuma gwamna Masari ya bayyana wasu daga cikin nasarorin da ya samu a cikin shekaru uku da rabi da ya hau karagar mulki musamman a bangarorin da ya ba mahimmanci A kananan hukumomi gudan biyun da aka kai ziyarar yakin zaben an karbi dubban ‘ya ‘yan jam’iyyar PDP da suka canza sheka zuwa jam’iyyar APC wanda shugaban jam’iyyar na jihar Shitu S. Shitu ya ce yanzu sun zama ‘ya ‘yan jam’iyyar APC babu banbanci da wadanda aka haifi jam’iyyar tare da su.

Sannan ya yi kira ga jama’a da su tabbatar sun zabi jam’iyyar APC a zabe mai zuwa domin ganin anci gaba da samun nasasar da aka sa gaba sabodda amfanin al’umma da kasa baki daya Kazalika gwamna Aminu Bello Masari ya buda hanyar da ta tashi daga mararrabar Sayaya zuwa garin mazoji mai tsawon kilomita 24 wanda daman tana cikin alkawuran da Masari ya dauka.

Source: hausa.leadership.ng


EmoticonEmoticon