Wednesday, 16 January 2019

Messi Ya Kafa Tarihin Da Babu Kamarsa A Laliga

Tags

Dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Barcelona, Leonel Messi, yakafa tarihin da babu wani dan wasa daya taba kafawa a gasar laliga tunb daga lokacin da aka fara buga gasar kusan shekaru sama da dari kenan.

Lionel Messi ya ci kwallaye 400 a gasar La Liga, bayan da Barcelona ta doke kungiyar kwallon kafa ta Eibar da ci 3-0 a wasan mako na 19 na gasar laliga da suka kara a ranar Lahadin da suka gabata.

Luis Suarez ne ya ci sauran kwallaye biyun daya bai wa kungiyar Barcelona damar samun maki biyar tsakaninta da wadda take mataki na biyu a teburin La Ligar bana wato kungiyar Atletico Madrid.

Da wannan kwallon da Messi ya ci ya tsawaita tarihin cin kwallaye a gasar ta La Liga bayan da dan wasa Cristiano Ronaldo ne keda kwallaye fiye da 300 a wasanni 435 da ya yi wa Real Madrid.

Messi wanda ya buga wa Barcelona wasa 22 a wannan kakar ta 2018 zuwa 2019 ya ci kwallaye 23, ciki har da kwallaye 17 da ya zura a raga a gasar La Liga, kuma shi ne kan gaba a ‘yan wasan da sukafi zuwa kwallo a kakar ta laligar Spaniya.

Barcelona za ta karbi bakuncin kungiyar kwallon kafa ta Lebante a wasa na biyu na gasar cin kofin Copa del Rey a ranar 17 ga watan Janairu, a wasan farko dai Levante ce ta yi nasara da ci 2-1.


EmoticonEmoticon