Wednesday, 16 January 2019

Duk Duniya Babu Kamar De Gea - Solskjaer

Tags

Mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Manchester United, Ole Gunnar Solskjaer, ya jinjina wa mai tsaren ragarsu, Dabid De Gea bisa gagarumar rawar da ya taka a nasarar da suka samu kan Tottenham a gasar firmiyar Ingila, in da suka tashi 1-0.

Solskjaer da ke zama kociyan rikon kwarya a kungiyar ya bayyana, De Gea a matsayin gola mafi kwarewa a duk fadin duniya, yayin da ya ce, mai tsaron ragar na kokarin kafa tarihin da za a ci gaba da tunawa da shi a Manchester United.

Mai tsaren ragar ya kawar da kwallayen da dama da Tottenham ta kai hare-harensu musamman bayan dawowa daga hutun rabin lokaci inda ya hana kwallaye 11 shifa ragar United din kokarin da shima kociyan Tottenham yace yakamata a jinjinawa mai tsaron ragar.

“Tabbas dole jinjinawa De Gea saboda abinda yayi a kungiyar ya nunawa duniya cewa kawo yanzu babu mai tsaron ragar daya kaishi iya tsare raga kuma ya cancanta daya lashe kyautar gwarzon mai tsaron raga na duniya” in ji Solkjaer.

Dan wasa Marcus Rashford ne ya jefa kwallo daya tilo a fafatawar ta ranar Lahadi kuma shima ya kafa tarihin zura kwallaye a raga a wasanni uku a jere yayinda kawo yanzu ya zura kwallaye hudu sannan ya taimaka an zura uku a lokacin Solkjaer.

Gabanin Solskjaer ya karbi aikin horar da Manchester Unted, akwai tazarar maki 8 tsakaninta da Arsenal, amma a yanzu kungiyar ta kulle wannan tazarar, in da kowacce daga cikinsu ke da maki 41.

Kocin ya samu nasara a dukkanin wasanni shida da ya jagoranci kungiyar tun bayan maye gurbin Jose Mourinho a cikin watan Disamba wanda kungiyar ta kora sakamakon rashin kokari yadda yakamata.


EmoticonEmoticon