Wednesday, 16 January 2019

Ba Za Mu Lamunci Sayen Kuri’a Ba –EFCC

Tags

Hukumar Yaki da Rashawa EFCC ta bayyana cewa, ba za ta amince da saye da sayar da kuri’a da wasu ‘yan siyasa su kan yi ba a yayin da ake gudanar da zabe ba, musamman a zaben dake tafe na 2019.

Mukadadashin shugaban sashin watsa labarai na hukumar, Mista Tony Orilade, ya bayyana haka a wani taro da aka yi wa lakabi da “Say No To Bote Buying” wanda aka gudanar a Abuja jiya Litinin.

Orilade ya ce, lamarin sayen kuri’a ya zama ruwan dare a tsakanin ‘yan siyasa na sayan kuri’u daga jama’a masu jefa kuri’a maimakon su je su nemi shawo kan ra’ayin su ta hanyar gabatar musu da bayanan akida da ayuyukan da za su gudanar gare su.

“Lallai wannan babban laifi ne kuma ba za mu amince da shi ba saboda a kwai babbar matsala tattare da sayen kuri’a daga hannun jama’a.

“I dan ka sayar da kuri’arka kamar ka sayar da rayuwar ka ne gaba daya har na tsawon shekara hudu kuma ba zaka iya yin korafi a kan yadda ake gudanar da mulki ba don ka riga ka sayar da ‘yancinka.

“Ku zabi mutanen da kuke da imani da abin da zai yi muku, ku zabi mutumin da kuke gani zai kare mutuncinku kuma zai kare dukkan abin da ya shafe ku da sauran ‘yan kasa,” inji shi.

Mista Usen Asanga, babban jami’i a kungiyar ‘Youth Alibe Foundation’, ya ce yaki da dukkan wani nau’in laifi aiki ne na kowa da kowa.

Asanga ya kuma kara da cewa, yadda ake ci gaba da sayen kuri’u a tsakanin jama’a, abin nau’in barazana ne ga tsarin dimokradiyya a Nijeriya.

“Idan muka sayar da kuri’armu to bamu da wani karfin gwiwar da zamu iya tambayar shugabanin a kan yadda suka gabatar da mulkinsu.

“Yana matukar mahimmanci mu zabi mutane da muke da yakinin za su kare mana ra’ayinmu ta haka kuma za mu iya tunkarar su akan yadda suke gabatar da ayuyukansu musamamman in sun kauce hanya,” inni shi.

Ya kuma bukaci hukumar zabe INEC ta tabbatar da ta gudanar da sahihin zabe wanda zai samu karbuwa ga dukkan ‘yan Nijeriya.

Tun da farko, shugaban shirya taron, Olanrewaju Toriseju, wanda aka fi sani da “Ambassador Wahala”, ya bukaci matasa su guji bangar siyasa a lokacin yakin neman zabe da lokacin gudanar da zabe da kuma bayan an kammala zaben gaba daya.

“Mun zo don tunatar da jama’a ne a kan illolin saye da sayar kuri’a ta hanyar kade kadekadenmu da kuma wasan kwaikwayo,” inji shi.

Toriseju, dan danwasan barkwanci ne kuma dan rajin kare hakkin bil’adama ne ya kuma ce an samu tallafin hukumar EFCC wajen gudannar da taron gangamin.

Source: hausa.leadership.ng


EmoticonEmoticon