Monday, 7 January 2019

ASUU Ta Amince Malaman Jami’a Su Yi Wa INEC Aiki

Tags

Kungiyar malaman jami’a, ASUU, ta tabbatar wa da hukumar zaben Najeriya, INEC, amincewarta kan malaman jami’a, wadanda mambobinta ne, cewa za su iya yi wa INEC din aikin zabe koda kuwa kungiyar ba ta daina gudanar da yajin aikin da ta ke yi a halin yanzu ba.

Wannan bayanin ya fito ne daga bakin hukumar zaben a karshen makon nan a wata sanarwa da ta bayar bayan kammala ganawa da shugabannin ASUU na kasa a hedikwatar kungiyar da ke Abuja.

Da alama wannan sanarwar babban albishir ce ga kasar, domin hakan zai rage fargabar da a ke da ita ta yiwuwar kawo cikas ga tafiyar da shirye-shiryen babban zabe na shekara ta 2019 da ke tafe a watan Fabrairu.

Idan dai za a iya tunawa, INEC ta saba yin amfani da malaman jamiar ne a lokacin manyan zabuka irin wadannan, inda ta ke nada su a matsayin manyan jami’an zaben nata a jihohin kasar, don tattaro ma ta sakamakon zaben da a ka kada.

“ASUU ta amince ta kyale mambobinta su yi aikin babban zaben 2019 a matsayin ma’aikata na wucingadi, duk da yajin aiki na kasa bakidaya da a ke yi a kasar,” in ji sanarwar INEC din.

Ta wara da cewa, “hakan ya biyo bayan rokon da shugaban hukumar, Farfesa Mahmood Yakubu, wanda ya jagoranci tawagar manyan kwamishihonin hukumar, kwararrun jami’ai da daraktoci na INEC, ya yiwa shugabancin kungiyar a hedikwatar ASUU da ke Jami’ar Abuja ranar Juma’ar 4 ga Janairu, 2019.”

Farfesa Mahmood ya nuna farin cikinsa kan wannan cigaba da a ka samu a lokacin da ya kai ziyarar, wacce tamkar ganin gidana, idan a ka yi la’akari da cewa shi ma malamin jami’a ne kuma wanda ya bayar da tasa gudunmawar ga cigaban ilimi a lokacin da ya ke rike da mukamin babban sakataren hukumar kula da gidauniyar manyan makarantu ta kasa (TETFUND).

A lokacin da ya ke rokon shugabannin ASUU din, Mahmood ya tunatar da su cewa daga ranar 4 ga Janairu zuwa lokacoin zabe kwanaki 42 ne kacal, kuma za a gudanar da zaben nan a mazabu 1,558 da akwatinan zabe har 119,973 da ke cibiyoyin zabe har guda 9,809 a fadin kasar cikin kananan hukumomi 774 da ke jihohi 36 na Najeriya da kuma babban birnin kasar Abuja.

Don haka sai ya nanata mu su cewa, wannan ba karamin aiki ba ne, wanda ya ke bukatar sadaukarwa daga kungiyar da kuma malaman su kansu.

A yayin da ya ke mayar da jawabi, shugaban ASUU na kasa, Farfesa Biodun Ogunyemi, sai ya tabbatar wa da hukumar cewa kungiyar ba za ta hana mambobinta shiga aikin babban zaben kasar ba.

Ya ce, “ASUU ba za ta taba yin wani abu wanda zai kawo cikas ga shirin babban zaben kasa ba, domin kungiyar a kullum ta na bayar da gudunmawarta ne ga wanzuwar dimukradiyya a Najeriya.

“Yajin aikinmu bai hada da INEC da babban zaben kasa ba. Zai zama daya daga cikin manyan laifuka ga sashen ilimi, musamman jami’o’in gwamnati mu shiga adawa da hakan. Haka zalika, yajin aikinmu ba zai shafi harkokin bincike da kyautata wa al’umma ba.

Ya kara da cewa, “dangantakarmu da INEC ta na nan tun gabanin mulkin shugabancin INEC na yanzu. Tsohon shugaban INEC, Farfesa Attahiru Jega, ya na shawartar ASUU kuma mun taimaka ma sa tun a zaben 2011.”

An dade a na fargabar ko yajin aikin da malaman jami’a su ke yi a Najeriya zai kawo cikas ko sauyi ga babban zaben kasar, amma a yanzu da alamu dai hakan ya kau.
Source: hausa.leadership.ng


EmoticonEmoticon