Monday, 7 January 2019

Gaskiyar Dangantakar Buhari Da Amina Zakari

Tags

A jiya Juma’a ce gwamnatin Nijeriya ta bayyana cewa, babu wata dangantaka ta jin tsakanin shugaban kasa Muhammadu Buhari da Amina Zakari wadda aka nada ta zama shugaban cibiyar tattara zaben shugaban kasa wanda za a yi a watan Fabariru mai zuwa.

“Shugaban kasa Buhari ba shi da dangantaka ta jini tsakaninsa da kwamishinar cibiyar tattara zaben shugaban kasa Amina Zakari,” Babban Mai taimaka wa shugaban kasa na musamman a kan harkokin yada labarai Malam Garba Shehu ne ya bayyana haka jiya Juma’a a Abuja.

“An dai samu auratayya ta nesa a cikin zuri’arsu amma cewa shugaban kasa na da dangantaka ta jini tsakaninsa da kwamishinar karya ce kawai,” inji shi.

In za iya tunawa dai an nada Amina Zakari ranar Alhamis din da ta gabata ta shugabanci Cibiyar tattara sakamakon zaben shugaban kasa a hukumar zabe mai zaman kanta wanda za a yi a watan Fabarairu mai zuwa.

Wannan matsayi da aka ba Amina ya tayar da kura a siyasar nijeriya, inda jam’iyyar adawa ta PDP ta nuna cewa, ita Amina ‘yar uwar Buhari ce, saboda haka suke zargin ya daukota ne ta yi masa aiki.

Sakataren watsa labarai na jam’iyyar PDP ya soki lamirin nadin Aminar inda y ace wannan kamar yi wa dimokaradiyya zagon kasa ne.

Shi kuma da yake mayar da martini kan wannan bayani, Malam, Shehu ya ce, wannan Magana da jam’iyyar ta PDP ke yi, Magana ce wadda bat a da tushe balle makama.

Source: hausa.leadership.ng


EmoticonEmoticon