Monday, 7 January 2019

Sojoji Sun Yi Wa Ofishin DailyTrust Dirar Mikiya A Abuja Da Borno

Tags

Jiya da yamma ne kwambar sojoji suka yiwa hedikwatar Media Trust, mawallafan jaridar DailyTrust da ke babban birnin tarayya, Abuja dirar mikiya.

Haka kuma makamancin wannan farmaki na sojojin Nijeriyan ya rutsa da ofishin yanki na kamfanin jaridar Daily Trust da ke Maiduguri, babban birnin jihar Borno, yayin da suka yi awon gaba da editan yanki- Uthman Abubakar da wakilin jaridar da ke jihar, Ibrahim Sawab.

Duk da ba a san dalilin da ya jawo daukar wannan mataki ba, amma ana alakanta matakin da wani rahoton da jaridar ta buga na ranar lahadi- dangane da yakin da sojojin ke yi a arewa maso-gabacin Nijeriya.

Kamfanin Daily Trust shi ne ya fitar da sanarwar samamen da yan sojan suka kai a ofishin ta- jim kadan da faruwar lamarin tare da karin bayani da cewa, sojojin sun wancakalar da kofar shiga ofishin ta na yanki ka ke Maiduguri, da karfin dawo-dawo, kana sun yi awon gaba da editocin ta guda biyu.

Wani ganau a wajen ya tabbatar da yadda ya ganewa idon sa zuwan sojoji a ofishin tare da yadda suka bukaci a hannunta musu editan lamurran siyasa a ofishin- Hamza Idris, wanda suka zarga da rubuta wancan labarin.
Source: hausa.leadership.ng


EmoticonEmoticon