Monday, 7 January 2019

Yan Bindigar Zamfara Na Da Alaka Da Boko Haram - Ministan Tsaro

Tags

Ministan Tsaro, Birgediya Janar Mansur Dan-Ali (mai ritaya), ya ce, ba za a iya yanke hukunci kan cewa babu alaka a tsakanin kungiyar ‘yan ta’addan Boko Haram da kuma ‘yan ta’addan da suke ta aiwatar da nau’ukan ta’addanci a Jihar Zamfara ba.

Da yake magana da manema labarai a ziyarar gani da ido da ya kai a Jihar ta Zamfara, Ministan cewa ya yi, a kowane lokaci, ‘yan ta’adda sukan nemi taimako ta wasu hanyoyin, ya kara da cewa, mahimmin abu dai shi ne mu samar da hanyar tsare kan iyakokin kasar nan.

Ya ce, ya zo ne domin ya gana da rundunonin da ke wajen domin sanin ainihin irin kalubalen da suke fuskanta da sauran matsalolin su domin sanin hanyar da ya kamata a bi. “Dawowa na kenan daga kasar Cadi, mun tattauna da su.

Mu na kan tattaunawa da kasashen da ke makwabtaka da mu, Nijar da Kamaru, domin tabbatar da tsaron kan iyakokinmu ta fuskacin kai da komowan makamai, wanda na tabbata yana da matukar mahimmanci a kan kalubalen ‘yan ta’adda a Nijeriya,” in ji shi.

A cewar sa, ko da za a kawo Sojoji milyan guda ne a Jihar, ba zai amfanar ba, har sai masu ruwa da tsaki na Jihar sun shirya hanyar neman zaman lafiya.

Ministan ya ce, kamata ya yi a ce an kafa rundunonin fararen hula ‘yan sa kai tun da jimawa, ba wai sai a yanzun ba, domin ai Sojoji ba su lakanci yanda wuraren suke ba sosai, hakan ne ya sanya ake kashe su, ba a horas da su a kan su yi kisa ba, su ma ai Mutane ne. An horas da Soja ne domin ya kawo zaman lafiya.”

Source: hausa.leadership.ng


EmoticonEmoticon