Tuesday, 8 January 2019

Ba Da Ni A Ka Yi Wa Buhari Ihu A Majalisa Ba – Dino Melaye

Tags

Sanatan nan da ake ta faman kwaramniya da shi, mai wakiltar mazabar Kogi ta Yamma, Sanata Dino Melaye, ya musanta rahotannin da kafafen yada labarai na yanar gizo suke yadawa da ke cewa yana daga cikin ‘yan Majalisun tarayyan da suka yi wa Shugaba Buhari, ihu a ranar 19 ga watan Disamba.

Wasu daga cikin ‘yan Majalisun na tarayya sun yi wa Buharin ihu a lokacin da yake gabatar wa da Majalisun kasafin kudin 2019, a wannan ranar, inda suka nemi su rika yin wasu kalaman batunci a gare shi.

Amma Melaye, wanda a halin yanzun yake farfadowa a wani Asibitin ‘yan sanda da ke Abuja, ya ce, ba zai yiwu a ce yana cikin wadanda suka aikata hakan ba, saboda shi ai ba ma shi a wajen zaman.

Cikin sanarwar da Sanatan ya fitar ta hannun mai taimaka masa ta fuskacin manema labarai, Gedion Ayodele, cewa ya yi, ba yana karyata hakan ne domin tsoron wani abu ba, sai dai don ya gyara gaskiyar maganar ce kadai.

A baya, Melaye ya ki ya karyata batun ne domin ya san tsegumi ne kawai irin na yanar gizo ba komai ba, amma ai Sanata Melaye, ba ma shi a cikin Majalisar sam a wannan ranar.

A kan radin kansa ne Sanata Melaye, ya gabatar da kansa ga ‘yan sanda a ranar Juma’a, bayan kwanaki takwas ‘yan sandan suna yi wa gidansa kawanya a Abuja.

A nan take kuma sai ya fadi kasa a some, inda aka yi gaggawan garzayawa da shi Asibitin na ‘yan sanda domin neman magani. Rundunar ‘yan sanda ta aike da jami’anta 60 a Asibitin da ke Garcia, Abuja, inda ake duba lafiyar ta Melaye.

Bayan da Likitocin Asibitin ne suka tsayu a kan Melaye, sai ya sami farfadowa, a bayan suman da ya yi jim kadan a fara masa tambayoyi a ofishin na ‘yan sanda da ke Guzape, Abuja.

Majiyoyi sun shaida wa wakilinmu cewa, jami’an kula da lafiyar na shi suna tunanin sai an yi masa gwajin, ‘cardiopulmonary,’ a sakamakon wasu abubuwan da Likitocin asibitin suka yi la’akari da shi.

Ana jin cewa, kila Liktan Asibitin ya bayar da shawarar a mayar da shi wani Asibitin kwararru inda suke da mahimman kayan aikin da za su iya kulawa da Melayen sosai.

Yan sandan sun ce ne, suna neman Melaye a bisa zargin da suke yi ma shi na harbin wani dan sanda mai suna, Sajan Danjuma Saliu, wanda ke aiki a sashen ‘yan sandan kwantar da tarzoma, bataliya ta 37, a sa’ilin da yake kan aikin tsayarwa da bincikar ababen hawa a kan titin, Aiyetoro Gbede, Mopa, Jihar Kogi.

Source: hausa.leadership.ng


EmoticonEmoticon