Tsohon shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa EFCC, Malam Nuhu Ribadu ya ce; zai tabbatar da cewa zaben 2019 da za a yi, shugaban kasa Buhari ya lashe jihar Adamawa da kashi 100. Ya ci gaba da cewa; a halin yanzu yana nan yana shiri yanan tuntubar masu fada a ji a jihar domin tabbatar da shugaba Buhari ya samu wannan nasarar a zaben da za a yi. Ribadu ya bayyana hakan ne a yau Litinin a garin Yola a lokacin da yake kaddamar da ba da motoci 40 na yakin neman zaben ga kungiyar ‘Black Cap Revolutionary Movement’ domin tabbatar da an gudanar da kamfen yadda ya kamata.
Ribadu ya bayyana cewa; jihar Adamawa jiha ce ta shugaba Buhari dari bisa dari. Kuma zai tabbatar da shugaba Buhari ya samu wannan nasarar a karo na biyu, saboda a cewarsa; shugaban ya dace a sake ba shi damar ya samu nasara a zaben da za a yi. “Ya kamata mu taimaki Buhari, domin ya ci gaba da ayyukan da ya faro ga Nijeriya.” Inji Ribadu.
Ribadu shi ne Daraktan gudanarwa na fage na kamfen din Buhari da Osinbajo na zaben 2019, ya jaddada cewa; Buhari zai samu ninkin kuri’un da ya samu a zaben 2015 a jihar Adamawa a wannan karon. Ya ce; idan Buhari a zaben 2015 ya samu kuri’u dubu 600 ne, to da yardar Allah a wannan zaben da za a yi zai samu kuri’u sama da miliyan guda a jihar Adamawa.
Source: hausa.leadership.ng

EmoticonEmoticon